Labarai

Kotun Ƙoli Ta Soke Shari’ar Hamza Al-Mustapha Kan Kisan Kudirat Abiola

Kotun Ƙoli ta Najeriya ta soke shari’ar tsohon Babban Jami’in Tsaro (CSO) ga Marigayi Shugaban Ƙasa Janar Sani Abacha, *Manjo Hamza Al-Mustapha* kan zargin kisan *Marigayiya Kudirat Abiola* matar Marigayi MKO Abiola.

 

Kudirat Abiola, wadda ita ce matar ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa, Marigayi MKO Abiola, wanda ake kyautata zaton ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yuni, 1993, wanda tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Babangida ya soke, an kashe ta ne a Legas a lokacin rikicin da ya biyo bayan soke zaɓen, yayin da take gwagwarmayar ganin an dawo da zaɓen.

 

Hukuncin da wata tawagar Alkalai biyar ta Kotun Ƙoli ta yanke, wanda Mai Shari’a Uwanni Aba-Aji ta jagoranta, ya kawo ƙarshen shari’ar da Gwamnatin Jihar Legas ta shigar a kan Al-Mustapha.

 

Kotun Ƙoli ta yanke hukunci gaba ɗaya cewa Gwamnatin Jihar Legas ta nuna rashin sha’awa a kan lamarin, kuma a sakamakon haka ta yi watsi da shi.

 

Mai Shari’a Aba-Aji ta bayyana cewa shekaru tara sun yi yawa ga mai ƙara (Gwamnatin Legas) don ta gabatar da sanarwar ɗaukaka ƙara da kuma takardun ƙarar.

 

Kotun ta nuna bacin ranta kan yadda Gwamnatin Jihar Legas ba ta tura wakilinta na shari’a ba, kuma ba a samar da wani bayani ga Kotun da wanda ake ƙara ba, duk da cewa an aiko musu da sanarwar sauraron ƙarar tun a shekarar 2020.

 

A bisa waɗannan dalilai, Kotun ta soke shari’ar gaba ɗaya.

 

NTA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button