INEC Ta Sanya Ranar Zaɓen Cike Gurbi a Kano

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen jihar Kano, ta ayyana Asabar, 21 ga Fabrairun shekarar 2026, a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano a ƙananan hukumomin Ungoggo da Birni.
Zaɓen na zuwa ne domin cike guraben kujerun majalisar da suka kasance babu kowa, sakamakon rasuwar ‘yan majalisar dokokin jihar guda biyu da ke wakiltar yankunan a baya-bayan nan.
A cikin sanarwar da ta fitar, INEC ta bayyana cewa an ɗauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe, tare da bai wa al’umma damar zaɓar wakilansu cikin ‘yanci da adalci.
Hukumar ta kuma bukaci jam’iyyun siyasa da su gaggauta miƙa sunayen ‘yan takararsu, tare da bin dukkan ƙa’idoji da sharuɗɗan dokar zaɓe kamar yadda kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe suka tanada.
INEC ta tabbatar wa al’ummar yankunan da abin ya shafa cewa za ta yi aiki tare da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro kafin, yayin da kuma bayan kammala zaɓen.




