Labarai

Haɗin Kai Ne Mabuɗin Kawo Ƙarshen Laifuka a Kano_ Baffa Babba Dan’Agundi

Darakta Janar na Cibiyar Inganta Ayyuka ta Ƙasa (NPC), Dr. Baffa Babba Dan’agundi, ya jinjina wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa ziyarar aiki da ya kai Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano da ke Bompai.

Gwamnan ya kai ziyarar ne domin yaba wa Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori kan ƙwarewar da jami’an ‘yan sanda suka nuna wajen kama waɗanda ake zargi da kashe wata mata da ‘ya’yanta shida a Ciranchi, Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

Dr. Dan’agundi ya bayyana cewa ziyarar Gwamnan za ta ƙara *ɗaga darajar jami’an ‘yan sanda tare da ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu,

Ya kuma jaddada cewa jagorancin CP Bakori ya kawo gagarumin ci gaba wajen inganta tsaro da dakile ayyukan laifuka a faɗin jihar Kano tun bayan da ya fara aiki.

Yayin da yake yaba wa salon shugabancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Dr. Dan’agundi ya siffanta shi a matsayin shugaba mai tawali’u da son talakawa wanda ke sauraron ra’ayoyin jama’a da kuma karɓar shawarwari masu ma’ana.

A ƙarshe, Dr. Dan’agundi ya nanata cewa, ziyarar ta Gwamnan ta nuna muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin tsaro.

Ya ce wannan haɗin kai ne hanya mafi inganci wajen kawo ƙarshen aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Kano, inda ya yaba da alƙawarin Gwamnan na ci gaba da aiki tare da CP Bakori.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button