Labarai

Daliban sashin Shari’a na Jami’ar Bayero Sun Ziyarci Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Zone One a Kano

Ziyarar, wacce aka gudanar a matsayin rangadin ban girma, ta bai wa daliban damar samun ilimi da fahimtar yadda sassa daban-daban na rundunar ‘yan sanda ke gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

 

A yayin ziyarar, daliban sun saurari bayanai daga shugabannin sassa masu muhimmanci, ciki har da:

* Sashen binciken manyan laifuka (CID), wanda CSP Ibrahim Usman Hamman ya wakilta.

 

* Sashen kula da harkokin kudi da mulki (DFA), wanda CSP Zakari Imam ya wakilta.

 

* Sashen gudanar da ayyuka na musamman (DOPS), wanda CSP Bashir Muhammed ya wakilta.

 

* Sashen tattara bayanan sirri (ZID), wanda Insfekta Chris Odang ya gabatar da jawabi a madadinsa.

 

Da yake jawabi a madadin daliban, shugaban kungiyar Equity Chambers, Ismail Ibrahim Awachi, ya nuna matukar godiyarsa ga rundunar ‘yan sanda bisa wannan dama da suka samu.

 

Ya ce, “Wannan ziyara ta bude mana ido kuma za ta kara mana ilimi da fahimta kan aikin dan sanda a Najeriya.”

 

A nasa bangaren, Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya, AIG Garba Ahmed, ya nuna farin cikinsa da wannan ziyara.

 

Ya kuma jaddada aniyar rundunar na ci gaba da hada kai da makarantu da sauran cibiyoyin ilimi domin karfafa aikin dan sanda na sa-kai da hadin gwiwa da al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button