Rundunar Ƴansandan Kaduna Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Sace Mutane Sama Da 160

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta janye sanarwar da ta bayar a baya na musanta garkuwa da mutane a ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru, inda a yanzu ta tabbatar da cewa lallai an sace mazauna garin da dama.
Wannan sauyin matsayar na zuwa ne kwanaki biyu bayan faruwar lamarin, wanda ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma suka daga ɓangarori daban-daban na al’umma da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam.
Yadda Lamarin Ya FaruA ranar Lahadin da ta gabata ne wasu miyagun ƴanbindiga suka far wa ƙauyen Kurmin Wali da misalin ƙarfe 9 na safe, lokacin da mazauna garin ke tsaka da gudanar da ibada a coci-coci daban-daban.Bayanai sun nuna cewa maharan sun zagaye garin tare da kwashe mutane daga coci-coci uku da suka haɗa da:1.Cocin Pentecostal Fellowship Assembly (PFA) ta ɗaya.2.Cocin Pentecostal Fellowship Assembly (PFA) ta biyu.3.Cocin Evangelical Church Winning All (ECWA).
Sarkin Kurmin Wali, Malam Ishaku Dan’azumi, ya tabbatar wa manema labarai cewa maharan sun tafi da mutane kusan 166. Ya bayyana cewa maharan sun zo ne a lokacin da mutane ke coci, suka zagaye su sannan suka tafi da su cikin daji.Haka shi ma shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen arewa, Joseph Hayab, ya bayyana cewa bayanan da suka samu sun nuna an sace mutane kusan 172, ko da yake wasu guda 9 sun samu nasarar tserewa daga baya.
Tun farko, rundunar ƴansandan ta fitar da sanarwa a daren ranar Litinin tana mai bayyana rahotannin garkuwar a matsayin “labaran bogi”, tana mai cewa ba ta da bayanan da za su tabbatar da hakan.Sai dai a wata sabuwar sanarwa da kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya fitar, ya bayyana cewa binciken sirri ya tabbatar musu da faruwar garkuwar.
Ya bayyana cewa rundunar ta riga ta tura jami’anta zuwa yankin Kajuru domin gudanar da aikin ceto.
kungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International ta soki matakin farko na hukumomin kasarnan na neman ɓoye gaskiyar lamarin.
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen garkuwa da mutane da ya zama ruwan dare a ƙasar.A halin yanzu,



