Labarai

Zargin Damfarar Filaye: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar da Sheikh Makwarari a Kotu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Isa Makwarari, a gaban Kotun Majistiri mai lamba 53 da ke unguwar Normansland a birnin Kano.

Ana zargin malamin ne da hannu a badakalar sayar da filayen gwamnati da na al’umma ba bisa ƙa’ida ba.

An gabatar da Sheikh Makwarari a gaban kotun, wadda Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti ke jagoranta, a ranar Talata, 20 ga watan Janairun 2026.

A yayin zaman kotun, lauyan wanda ake zargin ya bayyana cewa ba su shirya tsaf domin gabatar da shi ba, inda ya sanar da kotun cewa akwai wata shari’a makamanciyar wannan da ke gaban wata babbar kotu a jihar.

A nasa ɓangaren, lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Nura, ya shaida wa kotun cewa an fara shigar da ƙarar ne tun a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2025. Ya ƙara da cewa ‘yan sanda sun miƙa fayil ɗin shari’ar zuwa Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano domin neman shawarar lauya kan ko akwai isassun hujjoji da za a iya gurfanar da wanda ake zargin ko kuma a sallame shi.

Bayan sauraron bayanan ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti ya ɗage zaman kotun zuwa ranar Laraba, 21 ga watan Janairun 2026. A wannan rana ne ake sa ran za a karanto masa tuhume-tuhumen da ake yi masa a hukumance, sannan a saurari buƙatar belinsa.


Arewa update

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button