Labarai

DSS Ta Sake Damƙe Tsohon Atoni-Janar Abubakar Malami Kan Sabon Zargin Ta’addanci

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake cafke tsohon Atoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), jim kaɗan bayan an bayar da belinsa daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Majiyoyi daga hukumar sun tabbatar da cewa sabon kamen ya biyo bayan zarge-zargen da ake yi masa na hannu wajen samar da kuɗaɗen ayyukan ta’addanci.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa jami’an DSS sun yi wa Malami kofar rago ne a ranar Litinin, inda suka tasa ƙeyarsa da ya fito daga harabar gidan yarin bayan cika sharuɗɗan belinsa.

Jami’an Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Najeriya sun tabbatar da cewa an saki Malami bayan ya cika dukkan sharuɗɗan da kotu ta gindaya.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ƙoƙarin jin ta bakin hukumar DSS a hukumance ya ci tura.

Sakin Malami ya biyo bayan belin da Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayar a ranar 7 ga Janairu, 2026.

Kotun ta bayar da belin Malami, da matarsa, da kuma ɗansa a kan kuɗi naira miliyan 500 kowannensu, tare da wasu tsauraran sharuɗɗa.

Kafin wannan, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Malami, matarsa Asabe, da ɗansa a gaban kotu a ranar 29 ga Disamba, 2025, kan tuhume-tuhume 16 da suka shafi safarar kuɗaɗe da suka kai kimanin naira biliyan 8.7.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button