Labarai

Wasu daga cikin nasarorin sa Imam Abubakar Abdullahi yasamu kafun rasuwarsa

Al’ummar kasarnan na jimamin rasuwar Alhaji Abubakar Abdullahi, Babban Limamin Masallacin Akwatti da ke Nghar, Barkin Ladi a Jihar Plateau, wanda ya shahara da aikin ceton rayuka ba tare da nuna bambanci ba.

A lokacin rikicin Barkin Ladi na 23 zuwa 24 ga Yuni, 2018, Imam Abubakar ya buɗe masallacinsa da gidansa domin bai wa Kiristoci mafaka yayin da ake kashe-kashe.

 

Ya tsaya tsayin daka yana kare su, inda ya bayyana cewa dole ne a kashe shi kafin a cutar da waɗanda ke ƙarƙashinsa.

 

A kan wannan jarumta, an karrama shi da lambar yabo ta United States International Religious Freedom Award a shekarar 2019, kuma an shirya ba shi lambar girma ta ƙasa a Najeriya.

 

Mutuwarsa ta haifar da alhini a tsakanin Musulmi, Kiristoci da matasa, inda ake yabonsa a matsayin mutum mai tausayi da ya fifita ɗan’adamtaka sama da komai.

 

Tarihinsa ya zama darasi na zaman lafiya, haɗin kai da mutunta rayuwar ɗan Adam.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button