Kisan Dorayi: Gwamnatin Kano Za Ta Jagoranci Shigar da Ƙara’a gaban kotu

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ƴaƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin alhini.
A wata sanarwa da Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya fitar, gwamnatin ta bayyana kisan a matsayin mummunan aiki na rashin tausayi da ya saɓa wa doka ta bil’adama.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da tabbatar musu da cikakken goyon bayan gwamnati.
Gwamnatin ta yaba wa rundunar ƴansandan jihar bisa gaggawar matakin bincike da ya kai ga kama waɗanda ake zargi, tare da jaddada cewa za a gurfanar da su cikin gaggawa ta hannun Ofishin Babban Lauyan Jihar domin tabbatar da adalci.


