Labarai
Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce ta kashe ‘yan bindiga sama da 40 a wasu hare-haren da ta kai ta sama a jihar Borno

A wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar, ya ce an kai hare-haren ne a ranakun 15 da 16 ga watan Janairu a yankunan Azi da Musarram.
Sanarwar ta ce an kai harin ne bayan samun bayanan sirri game da yadda ‘yan bindigar ke shirin kai hari a garin Baga da wani wurin kamun kifi. Jiragen yakin sun kai dauki inda suka tarwatsa ‘yan bindigar, inda suka kashe sama da 40 daga cikinsu.
Rundunar ta ce wannan nasarar ta bai wa sojojin kasa damar kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu a yankin.




