Labarai

Kotu Ta Wanke Amaryar da Ake Zargi da Kashe Uwar Gidanta a Kano

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 13 da ke Miller Road ta wanke tare da sallamar Fatima Dahiru, amaryar da ake zargi da kashe uwar gidanta, Wasila Yunusa, a unguwar Farawa.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta ce ɓangaren gwamnati ya kasa gabatar da isassun hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da laifin kisan kai a kanta.

 

Fatima Dahiru an gurfanar da ita’a gaban kotu bisa tuhumar kisan kai tun bayan faruwar lamarin a watan Fabrairun 2019, inda tun daga farko ta musanta aikata laifin.

 

Gwamnati ta gabatar da shaidu bakwai, yayin da ɓangaren kariya ya gabatar da hujjoji domin kare wadda ake tuhuma.

 

Mai shari’a, bayan nazari kan dukkan shaidu da hujjojin da aka gabatar, ta sallami Fatima Dahiru bisa rashin gamsassun hujjoji daga ɓangaren masu gabatar da ƙara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button