Gwamnatin Kano Ta Musanta Rahoton Daily Najeriya

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta wani rahoto da wata kafar yaɗa labarai ta wallafa, wanda ke zargin cewa umarnin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar na dakatar da tura takardu zuwa ofishinsa ya janyo tsaiko ko durƙushewar harkokin gudanarwa a jihar.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar F. Ibrahim, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya mara tushe, tana mai cewa ba ya da hujjar doka ko gaskiya.
Sanarwar ta bayyana cewa an bayar da umarnin ne a ƙarshen watan Disamba, bayan karewar aikin kasafin kuɗin shekarar da ta gabata, yayin da sabon kasafin ke gaban Majalisar Dokoki.
Gwamnatin ta jaddada cewa manufar umarnin ba ta tsaya kan tsaida ayyukan mulki ba, sai dai ƙarfafa da’a da tsari a harkokin kuɗi, domin hana kashe kuɗaɗe ba tare da izini ba da kuma kare jihar daga matsalolin binciken kuɗi da shari’o’i a gaba.
Ta kuma tabbatar wa al’umma cewa ayyukan gwamnati, musamman a fannonin tsaro, lafiya, ilimi da tsafta, sun ci gaba da gudana yadda ya kamata bisa tanade-tanaden doka.




