Rundunar ’Yan Sandan Kano ta Dakile Yunƙurin Shigo da Abubuwan Fashewa da Miyagun Ƙwayoyi cikin jihar

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta samu gagarumar nasara wajen dakile yunƙurin shigo da abubuwan fashewa da kuma miyagun ƙwayoyi, tare da kama wani da ake zargi, a wasu ayyuka guda biyu da aka gudanar bisa bayanan sirri.
A cewar sanarwar rundunar, jami’an ’yan sanda daga Rijiyar Lemo Police Division sun kai samame a wani gida da ke Tudun Bojuwa, Karamar Hukumar Fagge, inda suka gano buhuna biyu masu ɗauke da roll-roll shida na detonating codes, da kuma fakiti 20 na ganyen da ake zargin tabar wiwi (Cannabis Sativa), da kuma sashe-sashe 220 na kwayoyin Exol.
Masana daga sashen EOD-CBRN na rundunar sun tantance kayayyakin, yayin da bincike ke ci gaba.
A wani aikin kuma, jami’an Anti-Daba Unit sun kama wani direban adaidaita sahu a unguwar Sani Mainagge, Gwale, dauke da jakunkuna uku masu ɗauke da detonators na lantarki guda 3,700.
Bincike ya kai ga cafke wani mutum mai suna Ibrahim Garba, mai shekaru 49, dan Jihar Zamfara, wanda ya amsa cewa yana taimakawa wajen jigilar kayayyakin daga Jihar Nasarawa zuwa wasu wurare.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da ayyukan, tare da kira ga jama’a da su kasance masu sa ido da kai rahoton duk wani motsi ko abu da ke da alamar haɗari ga ’yan sanda.




