Kwamishinan Lafiya na Kano Ya Karɓi Sabon Asibitin Kula da Lafiya a Matakin Farko a Garun Malam

Mai Girma Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, tare da tawagarsa, sun kai ziyara garin Dorawar Sallau da ke Karamar Hukumar Garun Malam, domin karɓar sabon asibitin kula da lafiya da aka kammala gininsa daga hannun ɗan kwangila.
Kwamishinan Lafiyar ya yabawa ɗan kwangilar bisa kyakkyawan aiki da ingancin ginin da aka yi. Ya bayyana cewa asibitin na daga cikin jerin Asibitocin Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHC) da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kano ke aiwatarwa tare da tallafin Babban Bankin Duniya (World Bank).
Dr. Yusuf ya bayyana cewa zuwa yanzu, Jihar Kano ta amfana da kusan asibitoci 187 na irin wannan, kuma ana sa ran adadin zai ƙaru nan gaba. Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na da shirin gina asibitoci 484, domin tabbatar da cewa kowacce mazaɓa a fadin jihar Kano ta samu aƙalla asibiti guda ɗaya.
A cewarsa, ana sa ran asibitocin za su rika aiki tsawon awanni 24 a kullum, domin sauƙaƙa wa al’umma samun ingantaccen kulawar lafiya a kusa da su, tare da rage wahalar yin doguwar tafiya neman magani.
Kwamishinan Lafiyar ya karɓi asibitin a madadin Gwamnatin Jihar Kano daga hannun wakilin kamfanin da ya aiwatar da aikin ginin, Lot6Obet-Obet Nigeria Limited, Injiniya Rabiu Shehu Yakubu.
Dr. Yusuf ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba, za a gayyaci Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, domin gudanar da bikin buɗe asibitin a hukumance.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Ci gaban Mazaɓa (WDC) na asibitin, Malam Idris Hamisu, wanda kuma shi ne Mai Unguwar yankin, ya bayyana farin cikinsa matuƙa bisa samun asibitin. Ya ce hakan zai taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa wa jama’ar yankin samun kulawar lafiya ba tare da sun yi nisa ba.
Malam Idris ya kuma ba da tabbacin cewa za su ci gaba da wayar da kan mata masu juna biyu domin su rika zuwa asibiti akai-akai don duba lafiyarsu, da nufin inganta lafiyar uwa da ta jariri a yankin.




