Siyasa

Hadimin Shugaban Ƙasa Ya Magantu kan Sauya Sheƙar Gwamnan Kano

Hadimin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Hon. Abdul’aziz Abdul’aziz, ya bayyana wani muhimmin bayani ta shafin sa na Facebook, inda ya yi tsokaci kan halin da ake ciki a fagen siyasar ƙasa.

 

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa.

Duk da cewa bai bayyana cikakken bayani kan lamarin ba, saƙon da hadimin shugaban ƙasa ya wallafa ya ƙara rura wutar muhawara a tsakanin ’yan siyasa da jama’a, musamman a Jihar Kano, inda batun sauya sheƙa ke ɗaukar hankalin al’umma.

Masu sharhi na ganin cewa duk wani mataki da gwamnan zai ɗauka a wannan lokaci zai yi tasiri mai zurfi ga tsarin siyasar Kano, duba da irin tasirin da yake da shi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button