Kwankwaso ba dan jam’iyyar NNPP bane domin yana cikin wadanda aka kora _ Sakataren Jam’iyya

Sakataren jam’iyyar NNPP na kasa, Ogini Olaposi, ya bayyana cewa dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai samu damar sake tsayawa takara a karkashin jam’iyyar a zaben 2027 ba.
Olaposi ya ce tikitin takarar shugaban kasa na NNPP a 2027 na ‘yan jam’iyya ne na gaskiya.
A cewarsa, Kwankwaso ya rasa damar sake neman tikitin jam’iyyar ne saboda wasu sabani da ba a warware su ba tsakanin jam’iyyar da kungiyar Kwankwasiyya.
Ya kuma yi zargin cewa wasu ayyuka na adawa da jam’iyya da wasu ‘yan kungiyar Kwankwasiyya suka yi bayan zaben shugaban kasa, ya kai ga korar manyan ‘ya’yan jam’iyyar, ciki har da Kwankwaso.
Olaposi ya kara da cewa, ba kamar zaben 2023 ba da aka bai wa Kwankwaso tikitin takara kai tsaye, jam’iyyar ta bullo da wani tsari na bude kofa gabanin zaben 2027, kuma tuni masu neman tsayawa takara daga gida da waje suka fara nuna sha’awarsu.



