Siyasa

Ganduje Ya Dawo Daga Dubai Domin Tuntubar Masu Ruwa da Tsaki Kan Siyasar Kano

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo Najeriya daga ƙasar Dubai domin fara jerin tuntuba kan halin da siyasar Jihar Kano ke ciki.

 

Jaridar Arewa Updates ta rawaito cewa wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatansa, Malam Muhammad Garba, ya fitar ga manema labarai.

 

A cewar sanarwar, Ganduje ya iso Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Asabar da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, inda daga bisani ya shirya wucewa Abuja da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

 

Sanarwar ta bayyana cewa tsohon gwamnan zai fara jerin tarurruka da tuntuba da shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki, domin duba sabon yanayin siyasar Kano da kuma yadda al’amura ke tafiya a jihar.

 

Haka kuma, ana sa ran Ganduje zai shiga aikin rijistar mambobin jam’iyyar APC ta hanyar intanet, wani shiri da jam’iyyar ta assasa domin sabunta bayanan mambobinta da kuma ƙarfafa tsarin tafiyar da ita.

 

Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da jita-jitar shirin Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, lamarin da ke ƙara ɗumama siyasar jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button