Kotu Ta Bada belin Malam Makwarari kan Naira miliyan 20

Kotun Majistrin ta ba da belin Malam Ibrahim Isa Makwarari kan Naira miliyan 20, bayan gurfanar da shi bisa zargin mallakar takardun filaye na bogi guda biyu.
An gurfanar da Malam Makwarari ne bisa zargin mallakar takardun fili guda biyu da ake zargin na bogi ne, waɗanda ke ɗauke da sunayen Alƙasim Usman Baba da Audu Danyaro Fagge.
Zargin ya samo asali ne daga ƙorafin da Ma’aikatar Kasa ta Jihar Kano ta shigar kan wani fili da ke kan titin Ahmadu Bello Way a Kano.
A yayin zaman kotun, Malam Ibrahim Isa Makwarari ya musanta zargin da ake masa.
Lauyansa, Barista A. T. Shehu, ya nemi kotu ta ba da belin sa, yana mai tabbatar da cewa za su gabatar da mutane sahihai da za su tsaya masa.
A nasa ɓangaren, mai gabatar da ƙara na gwamnati, Barista Nura A. Salisu, ya ƙalubalanci neman belin, yana mai cewa an daɗe ana neman wanda ake tuhuma tun watan Oktoba na shekarar 2025, amma ya ƙi amsa gayyatar ’yan sanda har sai da aka kama shi bayan samun umarnin kotu.
Ya roƙi kotun ta sanya tsauraran sharuɗɗa idan har za ta ba da belin.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, kotun ta amince da ba da belin Malam Makwarari kan Naira miliyan 20, tare da sanya sharuɗɗa masu tsauri kamar haka:
1. Kawo mutane biyu da za su tsaya masa.
2. Na farko zai kasance **Hakimin ƙaramar hukuma** tare da takardar amincewa daga masarauta.
3. Na biyu kuma **ɗan kasuwa** mai gida a Kano da ke da takardar mallaka.
4. Dukansu masu tsaya masa su liƙa hotunansu a jikin takardar karɓar beli.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu na shekarar 2026 domin ci gaba da shari’ar.




