Siyasa

Ƙungiyar Matasan Ijaw ta Ƙara Jaddada Kira ga Tinubu da ya Sauke Wike Daga Muƙaminsa

Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mista Alaye Theophilus, a lokacin da yake wani jawabi a birnin Fatakwal.

Mista Theophilus ya nuna rashin amincewar ƙungiyar da kakkausar murya kan abin da ya kira “yunƙurin da ba shi da tushe” na tsige Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, daga muƙaminsa.

A cewar shugaban, wannan yunƙuri na tsige gwamnan ya ci karo da muradun al’ummar Jihar Rivers waɗanda suka zaɓe shi.

Ya bayyana cewa, “Matakin tsige Gwamna Fubara tamkar cin amanar dimokuraɗiyya ne da kuma watsi da zaɓin da al’ummar jihar suka yi.”

Ƙungiyar ta bayyana matuƙar damuwarta kan rawar da Minista Wike ke takawa a siyasar jihar, inda ta jaddada cewa wannan ba shi ne karo na farko da ake nuna damuwa kan ayyukansa ba, wanda hakan ya sa ake ci gaba da samun kiraye-kirayen a sauke shi daga muƙamin minista.

Ya zuwa yanzu, fadar shugaban ƙasa ba ta ce uffan ba game da wannan sabon kiran da ƙungiyar ta Ijaw ta yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button