Majalisar Kano Ta Ce Sauya Sheƙar Gwamna Abba Yusuf Daga NNPP Na Iya Zama Dole

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana cewa rikice-rikicen shari’a da ke addabar jam’iyyar NNPP na iya tilasta wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran zababbun jam’iyyar sauya sheƙa domin kauce wa barazanar rasa muƙamansu.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini, ya ce rikicin shugabanci da hukuncin kotu da ke cikin NNPP na iya sa kotu ta yanke hukunci cewa ’yan takarar jam’iyyar ba su samu sahalewar tsayawa takara yadda doka ta tanada ba.
Ya yi gargaɗin cewa idan ba a warware matsalar ba, NNPP na iya fuskantar abin da ya faru da APC a Jihar Zamfara a 2019, inda kotu ta kwace dukkan muƙaman da jam’iyyar ta lashe.
Lawan Hussaini ya ce ana ci gaba da tattaunawa da Gwamna Abba Yusuf da jagoran jam’iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso, domin cimma matsaya kan ficewa daga NNPP cikin lumana, tare da la’akari da sauya sheƙa zuwa APC ko wata jam’iyya.




