Majalisar Dokokin Rivers Ta Fara Yunkurin Tsige Gwamna Fubara da Mataimakiyarsa

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers sun fara daukar matakin tsige Gwamna Siminalayi Fubara tare da Mataimakiyarsa, Ngozi Oduh, bisa zargin aikata matsanancin rashin gaskiya da saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Matakin ya biyo bayan wani zama na musamman da Majalisar ta gudanar a karkashin jagorancin Shugaban Majalisar, Martins Amaewhule.
A zaman, Shugaban Masu Rinjaye, Major Jack, ya karanta sanarwar tsige gwamnan wadda ’yan majalisa 26 suka amince da ita.
Sanarwar ta zargi Gwamna Fubara da aikata wasu munanan laifuka da ake ganin sun sabawa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki.
Shugaban Majalisar ya bayyana cewa za a mika wa gwamnan sanarwar cikin kwanaki bakwai, kamar yadda doka ta tanada.
Haka nan, Mataimakiyar Shugaban Masu Rinjaye, Linda Stewart, ta karanta wata sanarwa ta daban wadda ke dauke da irin wadannan zarge-zarge kan Mataimakiyar Gwamna, Ngozi Oduh.
Masu sharhi na siyasa na ganin wannan mataki na iya jefa Jihar Rivers cikin wani sabon yanayi na rikicin siyasa da shari’a, yayin da ake hasashen za a fuskanci gwagwarmaya mai zafi tsakanin bangarorin da abin ya shafa.
Tun da farko, TST Hausa ta ruwaito cewa jam’iyyar APC ta gargadi Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya daina tsoma baki a harkokin siyasar Jihar Rivers, ko kuma ya sauka daga mukaminsa idan siyasa ta fi masa muhimmanci.
Masu lura da al’amuran siyasa na danganta wannan gargadi da sabon salo da rikicin siyasar jihar ya dauka a halin yanzu.



