Hukumar Gidajen Yari Ta Kama Mutum Biyu Kan Yunkurin Shigar da Miyagun Ƙwayoyi Gidan a Kano

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta kasa reshen Jihar Kano, ta sanar da kama wasu mutum biyu da ake zargi da yunkurin shigar da ƙwayoyi da tabar wiwi cikin gidan yarin jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Musbahu Lawan, ya fitar, inda ya bayyana cewa an kama mutanen ne a lokacin da suke ƙoƙarin shigar da miyagun ƙwayoyin cikin gidan yari.
Sanarwar ta bayyana sunayen mutanen da aka kama Usman Khalid mai shekaru 25 da Bello Musa mai shekaru 24, waɗanda aka cafke su yayin da suke yunƙurin aikata laifin.
Hukumar ta yi gargaɗi ga jama’a kan duk wani yunƙurin shigar da haramtattun abubuwa cikin gidajen yari ko kuma shiga harkokin fursunoni, musamman a lokutan zirga-zirgar zuwa kotu, tana mai cewa irin wannan aiki na barazana ga tsaro kuma yana ɗauke da hukunci mai tsauri.
Sanarwar ta jaddada cewa aikin hukumar shi ne gyara hali da sauya tunanin fursunoni, don haka ba za ta lamunci duk wani yunkuri da zai lalata aikinta ba.
Hukumar ta ce ta bayar da umarnin miƙa mutanen da aka kama ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) domin ci gaba da bincike da daukar matakin da ya dace a kansu.
Ta kuma jaddada kudirinta na ci gaba da tabbatar da tsaro da kuma dakile ayyukan safarar miyagun ƙwayoyi a dukkan gidajen yari da kotuna da ke faɗin jihar Kano.




