Zargin Sace Ƴarinya: An Kai Ƙorafi Kan Wani Jami’in DSS Zuwa ga Gwamnati

‘Yan uwan wata ƙaramar yarinya ’yar shekaru 16 daga garin Haɗejia sun kai ƙorafi kan wani jami’in Hukumar DSS, bisa zargin sace yarinyar, riƙe ta tsawon lokaci tare da tilasta mata sauya addini, da kuma aikata mata fyaɗe har ta haihu.
Lauyan iyayen yarinyar, Barista Hussaini, ya bayyana cewa an gano inda yarinyar take ne bayan kusan shekaru biyu, a gidan wani jami’in DSS da ke zaune a barikinsu a Abuja.
A cewarsa, jami’in ya yi yunkurin tilasta wa iyayen yarinyar su aurar masa da ita, amma iyayen sun ƙi amincewa.
Barista Hussaini ya ce tun bayan gano lamarin, an kai ƙorafi ga Shugaban DSS, Fadar Shugaban Ƙasa, da kuma sauran hukumomin tsaro da shari’a, domin a gudanar da bincike mai zurfi tare da tabbatar da an bi wa yarinyar hakkinta bisa doka.
Lauyan ya jaddada cewa iyalan na neman adalci ne, tare da bukatar gwamnati ta ɗauki matakai masu tsauri domin dakile abin da ya kira munanan ayyukan satar yara, ɓoyewa da kuma tilasta musu sauya addini.
Ya bukaci hukumomi da su tabbatar da bin doka da oda, tare da kare rayuka da martabar ’ya’ya mata, musamman a yankunan Arewa.




