Labarai

MD karota ya Taya Gwamna Abba Kabir Yusuf Murnar Cika Shekaru 63 da Haihuwa

A cikin sakon taya murnar, Manajan Darakta na KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana cewa gwamnan ya kasance shugaba mai hangen nesa, adalci da kuma kishin jama’a, wanda manufofinsa ke ci gaba da kawo sauyi a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma a Kano.

Hon. Faisal Mahmud Kabir ya ce jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen aiwatar da gyare-gyare, samar da ci gaba da kuma shugabanci mai maida hankali kan jama’a, na daga cikin abubuwan da ke karfafa gwiwar ma’aikatan gwamnati wajen yin aiki tukuru domin ciyar da jihar gaba.

 

Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya kara wa gwamnan lafiya, tsawon rai, hikima da karfin guiwa domin ci gaba da jagorantar Jihar Kano zuwa tudun mun tsira.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button