Kwankwaso Ya Taya Gwamna Abba Kabir Yusuf Murnar Ranar Haihuwarsa Duk da Jita-jitar Sauya Shekar da akeyi masa

Jagoran jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar ranar haihuwarsa,
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), inda ya jaddada irin dangantaka da shekaru na aiki tare da suka yi a harkokin siyasa.
Sakon taya murnar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta yada jita-jita game da yiwuwar ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, lamarin da ke kara janyo hankalin jama’a da masu sharhi a fagen siyasa.
A cewar Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf ya taka muhimmiyar rawa a tafiyar siyasar Kano tun daga lokacin da ya fara aiki a matsayin mataimaki na musamman, zuwa mukamin kwamishina, har zuwa zama gwamnan jihar Kano.
Jagoran NNPP ya kuma yabawa gudunmawar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke bayarwa wajen ci gaban jihar Kano, musamman ta fuskar aiwatar da shirye-shiryen raya al’umma da bunkasa tattalin arziki.
Kwankwaso ya yi wa gwamnan addu’ar Allah ya kara masa lafiya, hikima da karfin zuciya domin ci gaba da jagorantar al’ummar Kano.




