Badaru Abubakar Ya Karyata Zargin Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar ADC

Tsohon Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya karyata labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa yana cikin tattaunawa domin sauya sheka zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Alhaji Badaru ya bayyana cewa labarin ba shi da tushe balle makama, yana mai cewa wata dabara ce ta yaudarar siyasa da nufin ruɗar jama’a da mambobin jam’iyya.
Ya jaddada cewa har yanzu yana nan daram cikin jam’iyyar APC wacce ya kasance daga cikin waɗanda suka taimaka wajen kafuwarta, tare da nuna cikakken biyayya da goyon baya ga jam’iyyar ba tare da wata tangarda ba.
Alhaji Badaru ya bukaci jama’a da mambobin APC da su yi watsi da irin waɗannan rahotannin ƙarya, yana mai tabbatar da cewa babu wani shiri ko niyyarsa ta barin jam’iyyar APC a wannan lokaci ko nan gaba.
Ya kara da cewa zai ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen ciyar da manufofin APC gaba domin ci gaban ƙasa da al’umma baki ɗaya.




