Zaɓen 2027: ADC Ta Sha Alwashin Magance Matsalar Tsaro a Arewa Maso Yamma

Jam’iyyar adawa ta ADC ta jaddada kudirinta na magance matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin, idan har ta samu damar karɓar ragamar mulki a zaɓukan shekarar 2027.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ADC na ƙasa mai wakiltar shiyyar Arewa maso Yamma, Malam Jafaru Sani, ne ya bayyana hakan
Malam Jafaru Sani ya ce jam’iyyar ADC ta tanadi tsare-tsare masu inganci da za su taimaka wajen shawo kan matsalar rashin tsaro a Arewa maso Yamma da ma ƙasar nan baki ɗaya, tare da yin gyare-gyare a ɓangaren shari’a domin tabbatar da adalci da zaman lafiya.
Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su rungumi sabuwar tafiya ta jam’iyyar ADC domin ceto ƙasar nan daga halin ƙunci da take ciki, wanda ya alakanta da gazawar jam’iyyar APC mai mulki.
A cewarsa, ADC jam’iyya ce mai hangen nesa da manufofi na gaskiya, tare da shugabanni masu jajircewa da za su iya kawo sauyi mai ma’ana a fannonin tsaro, tattalin arziki da adalci.
Jam’iyyar ta yi kira ga al’ummar Arewa maso Yamma da su haɗa kai da ita domin gina ƙasa mai tsaro, adalci da ci gaba mai ɗorewa, tana mai zargin jam’iyyar APC da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa da kuma cika alƙawuranta.




