Siyasa
Obi da Kwankwaso Na Tattaunawar Haɗin Gwiwa Domin Kalubalantar Atiku a ADC

Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na nazarin yiwuwar yin haɗin gwiwa domin kalubalantar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan tikitin shugabancin jam’iyyar ADC a zaɓen shekarar 2027.
Rahotanni sun nuna cewa wannan yunƙuri na zuwa ne bayan ƙoƙarin da aka yi na haɗa Obi da Kwankwaso gabanin zaɓen 2023, wanda ya ci tura sakamakon sabani kan wanda zai zama ɗan takara da mataimaki.
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ne ke jagorantar ƙoƙarin sulhunta shugabannin biyu, inda ake ganin akwai yiwuwar Rabiu Kwankwaso ya zama mataimakin ɗan takarar shugabancin ƙasa, Peter Obi.




