Labarai

Babu wanda ya dauko akidar Malam Aminu Kano na kishin jama’a kamar Gwamna Abba Kabir Yusuf

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya bayyana shi a matsayin magajin Malam Aminu Kano wajen kishin ci gaban Jihar Kano da talakawa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon taya murnar cikar Gwamna Abba Kabir Yusuf shekaru 63 a duniya, wanda kakakinsa, Bayo Onanuga, ya fitar.

 

A cikin sakon, Shugaban Ƙasar ya ce sauƙin kai, ƙasƙantar da kai da jajircewar Gwamna Abba sun bayyana a fili ta yadda yake tafiyar da harkokin mulki a Kano.

 

Tinubu ya ƙara da cewa yana da tabbacin gwamnan yana bin sahun siyasar Malam Aminu Kano wadda ta ta’allaka ne kan ci-gaba mai ɗorewa, bunƙasa al’umma tun daga tushe da kuma kare muradun talakawa.

Shugaban Ƙasar ya kuma yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan ayyukan ƙawata birnin Kano da suka haɗa da sabunta birane, gina tituna da gadoji a sassan jihar.

Haka zalika, Tinubu ya jinjina wa gwamnan bisa ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi, matakin da ya ce ya taimaka matuƙa wajen samun gagarumar nasara a sakamakon jarabawar NECO da ɗaliban jihar suka samu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button