Hatsarin Kwale-kwale Ya Hallaka Mutane 26 a Kogin Badin

Aƙalla mutane 26 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a Kogin Badin, tsakanin ƙauyen Adiyani da ke Ƙaramar Hukumar Guri a Jihar Jigawa, da kuma ƙauyen Garbi da ke Ƙaramar Hukumar Nguru a Jihar Yobe.
Cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Ƙaramar Hukumar Guri, Muhammad Umar Hadejia, ya fitar kuma aka bai wa thetentaclesnews.com.ng, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda suka mutu, mutane uku ‘yan ƙauyen Adiyani ne, yayin da 23 suka fito daga ƙauyen Garbi na Jihar Yobe
Da yake jawabi ga manema labarai bayan sallar jana’izar mutum ukun da suka rasu daga Adiyani, Shugaban Ƙaramar Hukumar Guri, Abubakar Umar Danbarde, ya ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare.
Danbarde ya bayyana cewa nan take majalisar ƙaramar hukumar, tare da haɗin gwiwar mazauna yankin, suka gudanar da aikin ceto, inda aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin kusa domin samun kulawar lafiya, kafin daga bisani a sallame su zuwa gidajensu.
Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma bayyana shirin majalisar na samar da na’urorin sufuri na ruwa na zamani, domin rage matsalolin sufuri da kuma kauce wa sake faruwar irin wannan hatsari a nan gaba.
Haka kuma, Danbarde ya sanar da shirin kafa dokar hana zirga-zirgar kwale-kwale daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe, domin ƙara tsaro, tare da roƙon jami’an tsaro su tabbatar da aiwatar da dokar.



