Siyasa

An Tsare Fitaccen Malamin Musulunci Bisa Zargin Yunkurin Juyin Mulki

Hukumomin tsaro sun tsare fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Khalifa Zariya, tsawon kwanaki 23 bisa zargin hannu a wani yunkurin juyin mulki ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama malamin ne a birnin Abuja, jim kaɗan bayan ya iso daga Zariya domin bin diddigin matsalar toshe asusun bankinsa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an danganta sunan Sheikh Khalifa da zargin ne bayan da aka gano musayar kuɗi Naira miliyan biyu tsakaninsa da wani jami’in soja da ake zargi da hannu a yunkurin kifar da gwamnati.

Sai dai, gwamnatin tarayya ta riga ta ƙaryata batun yunkurin juyin mulkin baki ɗaya.

Duk da haka, rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu ana tsare da malamin a hannun hukuma ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Iyalansa sun musanta duk wata alaƙa tsakaninsa da sojan da ake zargi, inda suka bayyana cewa kuɗin da aka turo masa an aika su ne domin neman addu’a da albarka, ta hannun wani daga cikin almajiransa da ke da sanayya da sojan.

 

Haka kuma, wasu daga cikin ɗalibansa sun shaida wa jaridar Premium Times cewa duk da cewa an tabbatar da cewa Sheikh Khalifa ba ya cikin jerin waɗanda ake zargi da yunkurin juyin mulki, har yanzu ana ci gaba da tsare shi ba tare da gabatar da wata hujja ta doka ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button