PDP Ta Yi Allah-wadai da Ficewar Gwamnan Plateau Zuwa APC

Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi Allah-wadai da matakin da gwamnan jihar Plateau ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar APC mai mulki.
Jam’iyyar ta bayyana cewa duk da ƙalubalen cikin gida da take fuskanta, bai kai ga a ce gwamnoninta na barin jam’iyyar domin komawa wata jam’iyya ba. Kakakin jam’iyyar ta ƙasa, Hajiya Farida Umar, ta shaida wa BBC cewa matakin gwamnan ya zo musu da mamaki da takaici.
Ta ce PDP ce ta karɓo jihar Plateau daga hannun APC, inda ta jaddada cewa ficewar gwamnan ba za ta hana jam’iyyar tsayar da ɗan takara a zaɓe mai zuwa tare da samun nasara ba.
Gwamnan ya sanar da komawarsa APC ne a ranar Juma’a, matakin da ke zuwa wata guda bayan ficewar wasu gwamnonin PDP daga jam’iyyar.
Bayan babban zaɓen 2023, PDP na da gwamnoni 12 a faɗin ƙasar, amma a halin yanzu huɗu ne kawai suka rage mata.




