Labarai

Jihar Neja Za Ta Sake Buɗe Makarantu Ranar 12 Ga Janairu

Gwamnatin Jihar Neja ta amince da sake buɗe makarantun furamare da na sakandiren jihar, bayan dakatar da su sakamakon matsalolin tsaro.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishiniyar Ilimin Furamare da Sakandire ta jihar, Hajiya Hadiza Mohammed, ta fitar, inda ta bayyana cewa an yanke wannan shawara ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimi.

A cewar sanarwar, za a sake buɗe makarantun ranar 12 ga watan Janairu domin ci gaba da harkokin koyo da koyarwa, sai dai makarantun da ke yankunan da ake ganin tsaro ya wadatar ne kaɗai za a buɗe.

Matakin na zuwa ne makonni kaɗan bayan makwabciyar jihar, Kebbi, ta sanar da sake buɗe makarantunta a ranar 5 ga watan Janairu.

Jihohin sun rufe makarantunsu tun a watan Nuwamba sakamakon hare-haren ƴan bindiga da aka kai wa wasu makarantu tare da sace ɗalibai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button