Siyasa

Bani da masaniya akan komawar Abba APC_ KWANKWASO

Jagoran jam’iyyar NNPP a kasarnan Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya barranta kansa daga duk wani yunƙurin komawa jam’iyyar APC tare da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki na tafiyar Kwankwasiyya da aka gudanar a ranar Juma’a.

A cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, an jaddada cewa Kwankwaso zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar NNPP, tare da yin watsi da dukkan rahotannin sauya sheƙa.

Sanarwar ta ƙara da cewa idan akwai wani mataki na gaba da zai ɗauka, Kwankwaso da kansa ne zai sanar, yana mai kira ga mabiyansa da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai.

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin komawa jam’iyyar APC a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button