Labarai

Abduljabbar Kabara Ya Nemi A Mayar Da Shi Gidan Yarin Kurmawa

Malam Sheikh Abduljabbar Kabara ya buƙaci hukumomi da mahukunta da su gaggauta mayar da shi gidan yarin Kurmawa da ke Kano, daga gidan yarin Kuje na Abuja, inda aka kai shi bayan sauya masa wuri.

A wata wasiƙa da ya rubuta a ranar 1 ga Janairu, 2026, Abduljabbar ya bayyana cewa an sauya masa gidan yari ne watanni uku da suka gabata ba tare da bin ƙa’ida ba, tare da hana shi ɗaukar muhimman takardun shari’arsa, waɗanda ya ce har yanzu suna gidan yarin Kurmawa.

Ya bayyana cewa rashin samun waɗannan takardu a hannunsa na jefa shi cikin damuwa, ganin cewa bai san halin da suke ciki ba, duk da cewa doka ta ba shi damar kula da takardunsa

Jagora t v tace BBC ta ruwaito cewa sakamakon haka, Abduljabbar ya yi kira ga hukumar kula da gidajen yari da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta mayar da shi gidan yarin Kurmawa inda aka tsare shi tun da fari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button