Labarai
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 7 a sabon harin da suka kai Plateau

Aƙalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hari wani ƙauye a Ƙaramar Hukumar Qua’an-Pan ta Jihar Plateau.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne a daren Juma’a a ƙauyen Bong da ke gundumar Doemak, inda maharan suka shiga gidaje suna kai farmaki ga mutanen da ba su samu damar tserewa ba.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun zo dauke da manyan makamai, inda suka kai hari kan mata, yara da tsofaffi.
Wani ɗan asalin yankin, Lawrence Dogari, ya shaida cewa mutane fiye da bakwai aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu har yanzu ba a gano halin da suke ciki ba.



