Rikici Ya Ƙara Tsananta a NNPP ta Kano

Siyasar Kano ta shiga wani sabon salo bayan da wani muhimmin taron caucus da Jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kira ya fuskanci kauracewa daga manyan jiga-jigan jam’iyyar. Taron, wanda aka gudanar a gidansa da ke Miller Road, ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga NNPP zuwa APC.
Rahotanni sun nuna cewa kusan dukkan sanatoci, ‘yan majalisu, kwamishinoni, shugabannin ƙananan hukumomi da shugabannin jam’iyya a Kano sun kaurace wa taron, abin da ke nuni da tsananin rarrabuwar kai a cikin NNPP.
A lokaci guda, wasu manyan jagororin jam’iyyar sun kai ziyartar goyon baya ga Mukaddashin Shugaban NNPP na jihar, Hon. Imam Zubairu Abiya, wanda ake ganin yana da goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Masu sharhi kan siyasa na ganin cewa wannan lamari ya ƙara ƙarfafa ra’ayin cewa ƙarfin ikon siyasa a NNPP ta Kano na ƙara sauyawa, lamarin da ke barazanar rugujewar jam’iyyar a jihar.



