Labarai

Sojojin Sun Ceto Mutane Shida da Aka Sace a Kaduna

Rundunar Sojin kasarnan ta sanar da cewa dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun samu nasarar ceto mutum shida da ‘yan bindiga suka sace a yankin Kajuru/Kujama na Jihar Kaduna.

 

A cewar wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X (Twitter), an gudanar da aikin ceton ne a ranar 5 ga Janairu, 2026, a matsayin wani bangare na jerin manyan ayyukan tsaro da ake ci gaba da yi a yankunan Chikun, Kajuru, Kachia da Kagarko, gami da al’ummomin da ke kusa da kan iyakar Kauru.

 

Sanarwar ta bayyana cewa aikin ya mayar da hankali ne kan takaita ayyukan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka da ke addabar yankunan.

 

Rundunar ta ce bayan samun kiran gaggawa kan motsin ‘yan bindiga a kusa da tsaunukan Kasso, sojojin da ke gudanar da aikin share fage a yankin Kujeni suka hanzarta zuwa wurin.

 

“Da isarsu, sojojin sun yi artabu da ‘yan bindigar, wanda hakan ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji. Dakarun suka bi sawunsu nan take, lamarin da ya kai ga samun nasarar kuɓutar da mutanen shida da aka sace,” in ji sanarwar.

 

Rundunar Sojin ta kara da cewa an mika mutanen da aka ceto ga wakilan ƙaramar hukumar Kajuru da kuma majalisar masarautar Kajuru, domin tabbatar da mayar da su hannun iyalansu lafiya.

 

Rundunar ta jaddada kudirinta na ci gaba da aiwatar da ayyukan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankunan da ke fuskantar kalubalen tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button