Da Ɗumi-ɗumi: Kwankwaso na Shirin Komawa ADC – Rahoto

Rahotanni da ke ta fitowa sun nuna cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP domin komawa jam’iyyar ADC.
Wata majiya ta kusa da Kwankwaso ta shaida cewa wannan mataki ya biyo bayan rikicin cikin gida da ke addabar NNPP, wanda ya kai matakin da ake ganin babu mafita, musamman dangane da shirye-shiryen tsayawa takara a zaɓukan da ke tafe.
Majiyar ta kwatanta halin da jam’iyyar NNPP ke ciki da abin da ya faru a wasu jam’iyyun siyasa irin su LP da PDP, inda rikice-rikice suka raunana tsarinsu har suka kasa tsayar da takara yadda ya kamata.
Rahoton ya ƙara da cewa rikicin ya ƙara tsananta ne bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna aniyarsa ta marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027 mai zuwa. Wannan mataki, a cewar majiyoyi, ya haifar da babban sabani tsakanin gwamnan da jagoransa na siyasa, Sanata Kwankwaso.
Majiyar ta bayyana cewa Kwankwaso ya sha alwashin ba zai koma jam’iyyar APC ba duk da matsin lambar siyasa, yayin da a nasa ɓangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf ke kallon komawa APC a matsayin hanya ta ƙarfafa alaƙa da gwamnatin tarayya.
Duk da Kwankwaso na da burin tsayawa takarar shugabancin Najeriya, goyon bayan da gwamnan Kano ya bai wa Tinubu ya ƙara zurfafa rarrabuwar kai a tsakaninsu, lamarin da ke ƙara ƙarfafa rade-radin sauya jam’iyya nan gaba kaɗan.




