Siyasa

Gwamnan Plateau Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta hanyar wasiƙa da ya aike wa shugabancin jam’iyyar ward ɗinsa na Ampang West, Mangu, a ranar 30 ga Disamba, 2025.

 

A cikin wasiƙar, Mutfwang ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu, amma ya bayyana cewa halin siyasar da ake ciki da burinsa na shugabanci mai ma’ana sun sa ya yanke shawarar neman wani dandali na siyasa daban. Gwamnan, wanda aka zaɓe shi a 2023 ƙarƙashin PDP, bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba.

 

Ficewarsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauye a jam’iyyun adawa, bayan komawar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, zuwa jam’iyyar ADC.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button