Ƴan Daba Sun Kashe Jami’in Civil Defence a Kano An yi jana’izar wani jami’in tsaron Civil Defence, Abdurra’uf Ali Ahmad Sharifai, wanda wasu da ake zargin ƴan daba ne suka kashe yayin da yake sintiri a Kano

Arewa Updates ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren bikin sabuwar shekara, a tsakanin titin gidan Zoo zuwa Court Road, lokacin da jami’an tsaro ke gudanar da sintiri domin yaƙi da ɓata-gari. A cewar bayanai, ƴan daban ne suka kai musu hari, inda suka kashe marigayin.
Marigayin Abdurra’uf Ali Ahmad Sharifai jami’i ne da ke aiki a ofishin Civil Defence na Sabilur Rashad da ke yankin Court Road ƴan kifi.
Game da wannan lamari, Arewa Updates ta nemi jin ta bakin Hukumar Civil Defence, amma zuwa lokacin haɗa wannan labari ba a samu wani bayani daga gare su ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun hare-haren ƴan daba a Kano ba.
A watan Oktoban da ya gabata ma, an yi zargin wasu ɓatagari da kashe Kwamandan Rundunar Yaƙi da masu ƙwacen waya a jihar.




