Labarai
Sabbin Dokokin Haraji: Ba Za a Cire Kuɗi Kai-tsaye Daga Asusun Banki Ba — Oyedele

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kasafi da Gyaran Haraji, Mista Taiwo Oyedele, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa sabbin dokokin haraji da za su fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, ba za su haɗa da cire kuɗi kai-tsaye daga asusun banki na mutane ba.
Oyedele ya bayyana hakan ne a wani shirin gidan talabijin na Channels, inda ya ce sabon tsarin haraji zai dogara ne kan yadda masu biyan haraji za su bayyana kuɗin shigarsu da kansu, ba wai sanya ido ko cire kuɗi ta ƙarfin tsiya daga banki ba.
Ya ƙara da cewa bayanin da ake yaɗawa game da cire kuɗi kai-tsaye daga asusun banki ba gaskiya ba ne, yana mai nufin kwantar da hankulan jama’a, musamman talakawa da masu ƙananan sana’o’i.



