Labarai
DG na NPC Ya Yi Alhinin Rasuwar Lauya Maryam Abubakar

Dakta Baffa Babba Dan Agundi, a madadin Ƙungiyar Lauyoyin Mata (Women Lawyers Congress – WLC), ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar Lauya Maryam Abubakar.
Marigayiyar, wadda ke riƙe da mukamin Darakta na Shirye-shirye a Cibiyar Wayar da Kai kan Adalci da Riƙon Amana (CAJA), kuma mamba a WLC, an bayyana rasuwarta a matsayin babbar rashi ga iyalanta, fannin shari’a da kuma al’ummar ƙungiyoyin fararen hula baki ɗaya.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Dakta Dan Agundi ya bayyana marigayiyar a matsayin ƙwararriyar lauya mai kishin adalci, riƙon amana, kare haƙƙin mata da kuma kyakkyawan shugabanci, tare da bayar da gagaruma ga harkokin Ƙungiyar Lauyoyin Mata.




