Siyasa

Cikakken dalilin da yasa Jam’iyyar N N P P ta kori shugabanta na Kano Dr Hashimu Sulaiman Dungurawa daga shugabancin jam’iyyar

Shugabannin Jam’iyyar NNPP na mazaɓar Gargari da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun sanar da korar Shugaban Jam’iyyar na jihar, Dr. Hashimu Sulaiman Dungurawa.

 

Ya ce sun ɗauki matakin ne bisa zargin cewa Dungurawa na tada fitina, korar muhimman ’ya’yan jam’iyya ba bisa ƙa’ida ba, da kuma zagin Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf.

 

Shugaban jam’iyyar na mazaɓar, Shu’aibu Hassan, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

 

Kazalika, sun zarge shi da ƙin halartar tarukan masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar, tare da zargin sa da yi wa jam’iyyar zagon ƙasa.

 

Shugabannin jam’iyyar sun ce ɗaukar wannan mataki ya zama dole domin kare martaba, tsari da mutuncin jam’iyyar NNPP a yankin.

 

Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ke fuskantar rikicin cikin gida, musamman dangane da raɗe-raɗin sauya sheƙar Gwamnan Kano zuwa jam’iyyar APC.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button