Asusun Tallafa wa Lafiya na Jihar Kano (KHETFUND) ya gudanar da taron duba ayyukan hukumomi da cibiyoyin da suka amfana da tallafin asusun a zango na uku da na hudu na shekarar 2025, domin tantance yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka fitar

A cewar Babbar Sakatariyar KHETFUND, Dakta Fatima Usman Zaharadeen, asusun ya raba sama da naira biliyan biyu ga hukumomi da cibiyoyin ilimi domin ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya da inganta samun kulawar lafiya ga al’ummar jihar.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya jaddada muhimmancin gaskiya da riƙon amana wajen amfani da kuɗaɗen, tare da yabawa KHETFUND kan yadda take tafiyar da harkokin kuɗi cikin tsari.
Haka zalika, wakilan KASLMA da Hukumar Kula da Lafiya ta Farko sun yaba da sakin kuɗaɗen kan lokaci, tare da kira da a ƙara mayar da hankali kan tallafa wa marasa galihu da masu buƙatar agajin gaggawa a asibitoci.
Taron ya ba da dama ga masu ruwa da tsaki su nazarci nasarorin da aka samu da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa don inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar Kano.


