Siyasa
ZAƁEN 2027: PDP Za Ta Iya Faɗuwa Idan Ba A Gyara Ba — Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike ya gargaɗi jam’iyyar PDP cewa tana fuskantar barazanar rashin nasara a babban zaɓen 2027 idan har ba ta magance rikice-rikicen cikin gida da suka addabe ta ba.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata tattaunawa da manema labarai a Port Harcourt. A cewarsa, shugabancin jam’iyyar na yanzu ya gaza mayar da hankali, sannan ba ya karɓar shawarwari masu ma’ana domin ceto jam’iyyar.




