Labarai

Rahotanni na cewa akalla ma’aikatan gidan Talabijin na Kasa NTA a jihar Gombe guda shida ne suka rasu, yayin da wasu uku suka jikkata, sakamakon hatsarin mota da ya faru a Jihar Gombe

Wadanda suka rasu sun hada da Manu Haruna Kwami, Manajan Gudanarwa da Zarah Umar, Manajar sashen Labarai; da Isa,wanda ya kasance Edita; da Musa Tabra, wanda ya kasance tsohon Manajan Labarai;da Aminu, shi kuma shine direba; da Adams, ma’aikacin Startimes.

Rahotanni sun bayyana cewa Emmanuel Akila (Manajan Labarai),da Jonathan Bara (Manajan Talla), da Steven Doddo (Babban Jami’in Talla) sun samu munanan raunuka kuma suna karbar kulawar likitoci

 

Shugabanci da ma’aikatan NTA Gombe na cigaba da nuna alhini da jimami kan wannan mummunan lamari, inda suka roki Allah Ya bada hakurin rashin su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button