NDLEA Ta Kama wanda ake zargi da Safarar Miyagun Ƙwayoyi

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta sanar da samun nasarar cafke wani mutum mai suna Chidiebere Basil mai shekaru 37, wanda ake zargi da kasancewa jagoran wata tawagar masu safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasashen ƙetare.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa an kama Basil ne tare da wasu mutane uku bayan wani bincike mai zurfi da jami’an hukumar suka gudanar a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas.
Jami’an hukumar sun fara ne da kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a shirin fitar da hodar iblis (cocaine) zuwa ƙasar Birtaniya.
Bayan gudanar da bincike a tsakanin waɗanda aka kama, an gano Basil a matsayin mutumin da ke jagorantar wannan haramtacciyar sana’a.



