Ketare

Najeriya ta jaddada goyon bayanta ga cikakken ikon Somalia

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sake jaddada cikakken goyon bayanta ga ikon ƙasa, haɗin kai da mutuncin yankunan Somalia, tare da gargaɗi kan amincewa da kowace ƙungiya ko yanki da ke neman ballewa.

 

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya na goyon bayan gwamnatin tarayyar Somalia a matsayin halattacciyar gwamnati, yana mai cewa duk wani yunkuri na amincewa da yankuna masu ballewa na iya haddasa rikici a yankin Horn of Africa.

 

Najeriya ta kuma yaba wa gwamnatin Somalia kan ƙoƙarinta na samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, tare da tabbatar da ci gaba da mara mata baya bisa tanadin Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Afirka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button