Labarai
Ƴansanda sun daƙile harin ƴan bindiga a Zamfara

Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ta ce ta daƙile yunkurin ƴan bindiga na kai hari a Ƙaramar Hukumar Maru a safiyar Lahadinnan bayan samun sahihan bayanan sirri.
Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana cewa haɗakar jami’an tsaro — ciki har da ƴansanda, sojoji, rundunar tsaron al’umma da ƴan sa-kai — sun fafata da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa da raunuka.
Sanarwar ta ce babu wanda ya mutu ko aka sace a yayin artabun, kuma an tsaurara matakan tsaro a Maru da yankunan makwabta.
Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya tabbatar wa al’umma da shirin jami’an tsaro na kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga jama’a su ci gaba da bayar da haɗin kai.



